A hukuncin da Kotun Kolin ta yanke, ta tabbatar da sahihancin zaben Okezie Ikpeazu a matsayin gwamnan jihar Abia.
Haka zalika kotun ta yi watsi da karar da aka shigar kan gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku inda ta tabbatar da shi a matayin gwamna.
Kotun ta bayyana cewa ta amince da hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben ta yanke inda ta ce jam'iyyar APC ba ta da dan takara a jihar a lokacin zabe.